Kasuwar S&P 500 ta fadi da kashi 1.2 cikin 100 yayin da sama da kashi 80 cikin 100 na hannayen jarin da aka rufe ya yi kasa. Kasuwar Dow Jones ta yi kasa da kashi 1.6 cikin 100.
Hakan na zuwa ne bayan da Trump ya yi shelar aniyar Apple ta zuba jarin biliyoyin daloli a Amurka yayin da yake kwarzanta nasarar tsarin harajin da ya zo dashi wajen bunkasa tattalin arzikin Amurka.
A cewar mujallar Forbes, dukiyar Dangote ta kusan ninka sau biyu, inda ta kai dala biliyan $23.9, wanda ya sanya shi a matsayi na 86 cikin jerin attajiran duniya.