Ku kasance da VOA Hausa kai tsaye kan zaben Najeriya na 2023 a VOAHausa.com.
Zaben 2023: Buhari Ya Koma Daura
Ana sa ran shugaba Buhari zai kada kuri’arsa a rumfar zabe da ke kusa da gidansa a garin Daura tare da mai dakinsa Aisha Buhari da sauran ahalinsa.
01:06Fabrairu 25, 2023
ZABEN 2023: Hukumar Kula Da Kafafen Yada Labarai Ta Amurka USAGM, Ta Horas Da ‘Yan Jarida Kan Tsare Dokokin Aiki
Hukumar kula da kafafen labarai na ketare ta Amurka wato USAGM, ta hori wakilan kafafen labaru na Najeriya kan yadda za su tsare dokokin aikin jarida idan sun tashi ba da labarai kan yadda za a gudanar da babban zabe har zuwa bayan sanar da sakamako.