Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka A Equatorial Guinea
Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka A Equatorial Guinea

1
Wata 'yar kallo ta shafa fenti na kalar tutar kasar Equatorial Guinea a lokacin wasan farko a tsakanin mai masaukin baki da kasar Kwango a garin Bata, asabar 17 Janairu 2015.(AP Photo/Themba Hadebe)

2
'Yan kallon kasar Mali su na tarbar 'yan wasan kasarsu a lokacin da suka isa babban filin jirgin saman Malabo, babban birnin Equatorial Guinea ran 16 Janairu 2015.

3
'Yan kallo sun cika makil a ranar farko a lokacin wasan farko a tsakanin mai masaukin baki da kasar Kwango a garin Bata, asabar 17 Janairu 2015.(AP Photo/Themba Hadebe)

4
Dan wasan Equatorial Guinea, Diosdado Mbele Mangue, a dama, yana kokarin tare dan wasan Kwango, Arnold Bouka Moutou, hagu,a wasan farko tsakanin kasashen biyu ran asabar 17 Janairu 2015