An shiga yini na biyu da Rasha ke ci gaba da sayar da makamai masu linzami kirar S- 400 ga kasar Turkiyya, lamarin da ka iya raunana dangantakar da ke tsakanin Amurka da Turkiyar.
ta daya fuskar kuma, hakan na sa sabuwar fasahar kera makaman sojin Rasha tana shiga hannun daya daga cikin manyan mambobin kungiyar tsaro ta NATO.
Ma’aikatar tsaron Turkiyya ta ce, a yau Asabar wani jirgin Rasha na hudu, ya sauke wasu karin sassan makaman na S-400 masu linzami a wani filin tashin jiragen sojin kasar da ke kusa da birnin Ankara.
Hakan na nufin, hukumomin kasar ta Turkiyya, sun yi watsi da barazanar da Amurka ta yi musu na kakaba masu takunkumi muddin ba su kaucewa sayen makaman ba.
A jiya Juma’a jirgin Rasha na farko ya isar da wasu sassan makaman, wandanda kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 2.2, lamarin da ya ja hankulan hukumomin Brussels da na Washington.