Birtaniya ta yi gargadi ga jiragen ruwan kasar masu safara akan teku da su kaucewa yankin Mashigin Hormuz “na dan wani lokaci” bayan da dakarun kasar Iran suka kwace wani jirgin dakon manta a wannan mashigi.
Bayan wani taron gaggawa da hukumomin Birtaniyar suka yi, wata mai magana da yawun gwamnatin ta ce, “Birtaniya na nuna matukar damuwarta kan irin halayen da Iran ke nunawa, wadanda ba za a amince da su ba.
Ta kara da cewa, halayen har ila yau, "sun fito karara suna tauye ‘yancin walwalar yin tafiye-tafiye akan teku.”
Hukumomin tsaron ruwan Iran sun ba da umurnin a kama jirgin ruwan na Birtaniya mai suna Stena Impero, saboda a cewarsu, “bai bi ka’idojin safara akan tekun ba.”
Iran ta kara da cewa, yanzu haka ta tura jirgin ruwan na Birtaniya zuwa gabar tekun Bander Abbas da ke kudanci kasar.