Burtaniya ta fara daukan matakan yadda za ta tunkari karancin samun kayayyaki amfani daga China, yayin da kamfanonin Chinan ke ta rufewa sanadiyyar barkewar cutar coronavirus.
Hukumomin kasar ta Burtaniya, na amfani ne da tsare-tsaren da suka tanada, ko da za su kammala ficewarsu daga kungiyar tarayyar turai ba tare da wata yarjejeniya ba.
Matakin na kuma zuwa ne, yayin da ake fargabar hukumomin Chinan za su rufe wasu birane tare da kamfanoni, yayin da cutar ta coronavirus ke ci gaba da yaduwa.
Wannan lamarin dka iya haifar da karancin kayayyakin amfani, kamar na asibiti da sauran kayayyakin na yau da kullum a Burtaniyar.
Yanzu haka an bukaci kamfanonin Burtaniyar da dama, da su nemi wasu hanyoyin samun wadannan kayayyaki.
Hakan dai na faruwa ne yayin da hukumar lafiya ta duniya WHO, ta fara daukan matakan ganin cutar ta coronavirus ba ta shiga nahiyar Afirka ba.
"Mun fahimci cewa, kasashenmu sun samar da matakan kariya sanadiyyar annobar cutar Ebola da ta barke a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, saboda haka, wannan shiri, shi ake amfani da shi wajen tunkarar cutar ta coronavirus.” Inji Matshidiso Moeti, Darektar a Hukumar ta WHO, wacce ke kula da nahiyar ta Afirka.