Yayin da adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar coronavirus ya haura 1000, hukumomi a China sun kori wasu manyan jami’an kiwon lafiya biyu daga mukamansu a Lardin Hubei, inda cutar ta fi kamari.
A yau Talata kafar yada labaran kasar ta Sin ta ruwaito cewa, an sallami Kwamishinan Lafiya a lardin na Hubei, Zhang Jin da kuma Liu Yingzi, Darekta a ma’aikatar ta lafiyar.
Sallamar wadannan manyan jami’ai na zuwa ne, kwana guda bayan da aka samu karin mutuwar mutum 103 a lardin na Hubei, inda aka rufe miliyoyin mutane a gidajensu, a kuma daidai lokacin da ake korafin samun matsalar karancin abinci a yankin.
Ya zuwa yanzu, gwamnatin ta China ta tabbatar da cewa mutum 43,000 ne suka kamu da cutar.
A jiya Litinin, Shugaba Xi Jinping ya ziyararci wasu da suka kamu da cutar ta coronavirus a wani asibiti da ke Beijing, kamar yadda rahotanni suka nuna.
A wani karin rahoto game da ci gaba da yaduwar cutar coronavirus a kasar ta China, dubban dalibai ‘yan nahiyar Afirka da ke karatu a kasar, suna fatan ganin gwamnatocinsu sun kwashe su daga kasar.
Solomon Yohanna, wani dan kasar Habasha, da ke karatu a fannin kere-keren zamani a jami’ar Wuchang da ke yankin Wuhan, wato inda cutar ta fi kamari, ya ce dukkan daliban jami’ar 15,000 sun fice daga makarantar.
A cewar shi, akwai daliban kasashen waje kusan 200 da suka rage a makarantar, mafi aksarinsu ‘yan nahiyar Afirka.
Wani dalibi daban wanda shi ma dan kasar ta Habasha ne, ya yi kira ga gwamnatin kasarsu da ta aika a kwashe su.
Kiyasi dai ya nuna cewa, akwai akalla ‘yan Afirka 61,000 da ke karatu a kasar ta China.
A halin da ake ciki, suna fuskantar matsalar karancin abinci tare da zama cikin yanayi na rashin tabbas.
Facebook Forum