Real Madrid ta kama abokiyar hamayyarta Barcelona a wasan hammaya na El Classico ta lallasa ta da ci 2-1.
Dan wasan Madrid Karim Benzema ne ya fara zura kwallo ta farko a minti na 13 sai Toni Kroos ya kara wata kwallon a minti na 28 a wasan, wanda aka buga a filin Alfredo di Stefano.
A ranar Talatar da ta gabata, Madrid ta doke Liverpool da ci 3-1 a gasar neman lashe kofin zakarun turai.
Sai dai dan wasan Barcelona Oscar Mingueza ya samu nasarar jefa kwallo daya a minti na 60 ya kuma yi yunkurin karawa amma abin ya cutura.
Amma Casemiro na Madrid ya fita a wasan, bayan da aka ba shi katin gargadi a karo na biyu, wanda ya janyo mai jan katin sallama.
‘Yan wasan Ronald Koeman sun yi amannar an danne musu bugun fenarti a lokacin da aka ka da Martin Braithwaite, bayan wata shigar karfi da suke zargin Ferland Mendy ya yi masa.
Yanzu yaran Zinedane Zidane sun haura saman teburin gasar ta La Liga inda suka yi kunnen doki da maki 66 da Atletico Madrid, wacce ake ganin za ta iya kwato mukaminta na zama a saman teburin, idan ta hadu da Real Betis a ranar Lahadi ta samu nasara akanta.
A ranar 14 ga watan Afrilu, Madrid za ta kai wa Liverpool ziyara a wasan zagaye na biyu na quarter-final a kokarin neman lashe kofin zakarun turai na UEFA.