Wasu mahara su uku sun kai harin da ya kashe mutane fiye da 40 a filin jirgin saman Ataturk na Istnabul a Turkiyya, daya daga cikin filayen jiragen saman da suka fi cika da jama'a a fadin duniya.
Harin Kunar-Bakin Wake A Filin Jirgin Saman Istanbul

1
Iyalan daya daga cikin mutanen da suka mutu a harin na filin jirgin saman Istanbul Ataturk su na tsaye a kofar wani dakin ajiye gawa a Istanbul, laraba 29 Yuni, 2016.

2
Gawarwaki a kofar filin jirgin saman Istanbul Ataturk a bayan tashin bam na kunar bakin wake talata 28 Yuni, 2016.

3
Motocin daukar marasa lafiya da gawa a filin jirgin saman Istanbul Ataturk, a Turkiyya

4
'Yan sanda su na yin sintiri Laraba 29 Yuni, 2016 a filin jirgin saman Istanbul Ataturk, mafi girma a kasar Turkiyya, bayan harin bam na ran talata.