A wasan k,arshe da aka buga a gasar lashe kofin duniya ta Confederation Cup a kasar Rasha, Jamus ta doke kasar Chile da ci 1-0.
Jamus Ta Lashe Kofin gasar Confederation Cup Ta Duniya A Kasar Rasha

1
'Yan wasan kwallon kasar Jamus na murna bayan da suka lashe kofin gasar nahiyoyi na wannan shekarar 2017 a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli na shekarar 2017 a garin Saint Petersburg dake Rasha.

2
Kafin a fara wasan karshe tsakanin Jamus da kasar Chile a gasar nahiyoyi ta Confederation Cup 2017 a ranar Lahadi 2 ga watan Yuni na shekarar 2017 a garin Saint Petersburg dake Rasha.

3
Dan wasan Brazil Ronaldo rike da kofin gasar ta Confederation Cup yayin da ake bikin rufe gasar a birnin St. Petersburg dake Rasha

4
'Yan wassan kwallo kafa na kasar Chile kafin a fara wasan karshe a babban fili na wasanni dake garin Saint Petersbourg dake Rasha a ranar Lahadi 2 ga watan Yuni shekarar 2017.
Facebook Forum