Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwantiragin Messi a Barcelona Ya Kai Dala Miliyan 673 - Rahoto


Messi
Messi

Wani rahoto da aka wallafa, ya nuna cewa kwantiragin Lionel Messi a Barcelona na tsawon shekara hudu ya kai euro miliyan 555.2 ko dala miliyan 673.8.

Jaridar El Mundo ta kasar Spaniya ce ta wallafa rahoton a ranar Lahadi wanda ya nuna kwantiragin da Messi ya sa hannu akai a watan Nuwambar shekarar 2017 ya kai wannan makudan kudade.

Idan dai har farashin ya tabbata, hakan na nufin, wannan shi ne kwantiragi mafi tsada da aka biya wani dan wasan.

Kididdga ta nuna cewa, hakan na nufin ana biyan Messi dan shekarar 33 dala miliyan 168.5 a duk kakar wasa kenan, kuma bisa dokar kasar Spaniya, ya zama wajibi ya biya kusan rabin wadannan kudade a matsayin haraji.

A watan Yunin wannan shekara kwantiragin zai kawo karshe.

A kuma watan Agustan da ya gabata, ya mika bukatarsa ta barin Barcelona, lamarin da ya girgiza duniyar kwallon kafa. Amma ba a sani ba ko zai sake sabunta wannan kwantiragi.

Fitowar wannan rahoto na zuwa ne yayin da Messi ya ci wa Barcelona kwallo ta 650 yayin karawar da suka yi da Athletico Bilbao a gasar La Liga a ranar Lahadi.

Ya sha kwallon ne da bugu mai tazara da aka ba shi inda aka tashi a wasan da ci 2-1.

Abubuwan Bajinta Biyar Da Har Yanzu Lionel Messi Ke Zarra Kai
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:40 0:00


Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG