Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester City Na Saman Tebur, Sheffield Ta Batawa Man U. Gari


Pep Guardiola, Kocin Manchester City
Pep Guardiola, Kocin Manchester City

Manchester City ta zama club ta tara da ta zauna a saman teburin gasar Premier a wannan kakar wasa.

A bayan-bayan nan Manchester United ce a saman teburin.

Hakan na zuwa ne bayan da City ta doke West Brom da ci 5-0 a wasan da suka kara a ranar Talata.

Sai dai kocin City Pep Guardiola ya yi ikrarin cewa, ba zama a saman teburin ne bukatar da take gabansa ba a yanzu.

Hakazalika yawan kwallaye da Manchester City take da su musamman wadanda ta samu a karawarta da West Brom sun taimaka mata wajen yin zarra a gasar

Da a ce Manchester United ta doke Sheffield a wasansu na ranar Laraba, da ta koma matsayinta na farko, amma ta sha kashi a hannun Sheffield din da ci 2-1.

Masu sharhi kan kwallon kafa na nuni da cewa, wannan karba-karba da ake yi na zama a saman teburin gasar, alama ce da ke nuna cewa, da wuya a iya hassashen wanda zai lashe kofin a bana.

Yanzu City na da maki 41 a saman teburin, Manchester United na biye da ita da maki 40 sai Leicester City mai maki 39.

West Ham na matsayi na hudu da maki 35 yayin da Liverpool da ke rike da kofin gasar take da maki 34 a matsayin na biyar.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG