Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da ministocin makamashi na kasashen Najeriya, Nijar da kuma Aljeriya su ka fitar a hukumance a birnin Algiers na kasar Aljeriya sun yi shelar rattaba hannu kan shirin shimfida bututun iskar gas daga Najeriya zuwa Turai
Tun a shekara ta 2009 kasashen uku suka kaddamar da shirin mai suna projet gazoduc trassaharien. Shirin ya tanadi shimfida bututu domin fitar da isakar gas din Najeriya zuwa Turai domin sayarwa.
Bututun mai tsawan kilomita 4128 zai ratsa tashi daga Najeriya ya ratsa Nijar zuwa kasar Aljeria, inda zai hadu da bututun jigilar iskar gas na Aljeriya zuwa Turai
Tun daga wancan lokacin ya zamo shafa labari shuni to saidai farfado da wannan yarjejeniya da ministocin kasashen Najeriya, Nijar da Aljeriya mai masaukin baki su ka yi, na zuwa ne mako biyu da ficewar Nijar daga kungiyar ECOWAS ko cedeao lamarin da masana irin su Abdourahamane Dikko ke ganin fitar Nijar daga ECOWAS ba zai shafi wannan aikin ba.
Rikicin Ukraine da Rasha ya haifar da bukatar iskar gas a Turai wanda ya sanya kasashen uku farfado da wannan tsohuwar yarjejeniyar wanda tuni masana tattalin arziki irin su malam Aminu su ka bayyana irin alfanun da Nijar za ta samu acikin wannan aiki na bututun gas zuwa Turai.
Kungiyoyin kare muhalli, ta bakin Abubakar Nafi’u, sun bukaci gwamnatin Nijar da ta kula domin ganin an kiyaye muhalli a cikin aikin.
An kiyasta cewa aikin gina bututun zai lakume miliyan dubu goma sha uku na dalar Amurka kuma zai samar da dala miliyan dubu talatin ga kasashen a kowace shekara. To saidai kawo yanzu kasashen ba su sanar da lokacin soma wannan aikin ba da kuma lokacin kammala shi.
Saurari cikakken rahoton Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna