Shugaban na Amurka, ya fada a shafin kafar sadarwar zamanin shi na Truth Media cewa, ‘’mun san akwai karin dalibai a jami’ar Columbiya da sauran jami’o'i a sassan kasa da dama da suka tsalma kan su a zanga-zangar nuna goyon baya ga 'yan ta'adda, da masu kin jinin Yahudawa, da harkokin Amurka, lamarin da Gwamnatin Trump ba zata lamunta ba.
Jami’an shigi da ficin Amurka ne suka kama Khalil a karshen makon da ya gabata. Yana daya daga cikin na gaba gaba a yayin zanga-zangar da ta barke a Columbia da wasu harabobin jami’oi a bara domin adawa da yakin da Isra’ila ke yi da kungiyar da Amurkan ta aiyana da ta ta’addanci ta Hamas a Gaza.
To amma a mafi yawan bangarori, zanga-zangar ta kai karshe ne, kuma ba ta sake tashi ba, a lokacin da aka koma karatu a farkon shekarar karatu na bazarar da ya gabata.
Ma’aikatar tsaron cikin cikin gida ta ce, kamun da akaima Khalil mara baya ne ga umurnin shugaban kasa na shugaba Trump da ya haramta nuna kin jinin Yahudawa, da hadin guiwa da ma’aikatar cikin gida.
Khalil wanda aka dauki bayanan sa a matsayin dan kasar Syria, ya samu digiri na biyu a fannin harkokin kasashen ketare a shekarar karatun bara daga jami’ar Columbiya. A lokacin da aka kama shi yana da takardar shedar zama a Amurka da ake cewa, Green Card. Kamar yadda kungiyar dalibai ma’aikata na Columbiya ta bayyana, yana auren ba’amurkiya dake dauke da juna biyu na watanni takwas.
Ba a dai zarge shi da aikata wani laifi ba da ya karya doka.
Trump ya rubuta a wata wallafa a kafar sadarwar zamani cewa, ‘’idan kana goyon bayan ta’addanci, da ya hada da kisan maza, mata da yaran da ba su ji ba ba su gani ba, kasancewar ka a nan ta yi hannun riga tsare tsare da muradun mu, don haka bama maraba da kai a nan. Muna sa ran duk wanda ke cikin kwalejoji da Jami’oin Amurka ya kiyaye hakan.’’
Dandalin Mu Tattauna