Faransa ta ce za ta toshe duk wata kofa da za ta ba da damar a cimma matsayar cinikayya tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da Brazil, yayin da ake ci gaba da ta-da jijiyar wuya sanadiyyar wutar dajin da take ci gaba da ruruwa a katafaren dajin nan na Amazon mai danshi da koramu.
Wata sanarwa da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya fitar a jiya Juma’a, ta nuna fushin hukumomin nahiyar ta turai, kan kalaman da Brazil ke yi a ‘yan makonnin nan, wadanda suke nuna karara cewa, shugaban kasar Jair Bolsonaro, ba ya mutunta alkawarin da ya yi kan sauyin yanayi.
Kungiyar ta EU ta kuma nuna damuwa kan batun nau’ukan halittun da ke rayuwa a dajin wadanda wutar za ta shafa.
Shi dai wani yanki na dajin na Amazon na kasar ta Brazil ne, yayin da wani sashinsa ke sauran kasashen da ke yankin kudancin Amurka.
Dubban curin-curin wutar dajin da ke ci gab da tashi a dajin na Amazon, na barazana ga dajin da dumbin halittun da ke cikinsa.
A jiya Juma'a kasar ta Brazil ta bayyana shirinta na tura dakaru domin kashe wutar da ta mamaye dajin.