Shugaban kwamitin bada shawarwari kan sha'anin addini Farfesa, Sambo Waleed Junaidu ne ya sanyawa sanarwar hannu
WASHINGTON, DC —
Majalisar Sarkin Musulmi Abubakar Saad na uku ta fitar da sanarwa game da lokacin da ya kamata a fara neman ganin watan sallar azumi.
Wakilin Sashen Hausa a Sokoto Murtala Faruk Sanyinna yayi karin bayanin sanarwar a wata tattaunawa da babban editan Sashen Hausa Aliyu Mustapha.
Your browser doesn’t support HTML5
Daga daren yau asabar za a fara neman ganin watan Sallah - 2':49"
Kafin sanarwar ta Fadar Sarkin Musulmi tuni har mutane sun fara aikawa juna da wasu sakonni masu rudarwa game da ganin watan na sallar azumi.