Hotuna Daga Sassan Duniya Daban Daban
Mazuna yankin Hanoi, a kasar Vietnam, sun gamu da ambaliyar ruwan sama
 
Dakarun Rudunar Adawar Kasar Syria wanda ake kira SDF suna murnar nasarar da suka samu akan mayakan kungiyar ISIS
 
Wata mata na tsikar furanni domin ta siyar da su a kasuwar bikin Diwali a Nepal
 
Wani mamba na kamfanin Chirstie's Hong Kong na baje kolin wata jakar hanu da aka kayata lu'u- lu'u guda dubu daya da daya
 
Dakarun kasar Philippines a hanyar su ta komawa masauki bayan shugaba Rodrigo Duterte ya ayana yancin kan Yankin Marawi na kasar  Philippines
 
Manoma na tafiya da dabbobinsu a gefen wata fadama a kasar Spaniya
 
Wani mazaunin kauyen Galicia, na duba wurin da wutar daji ta cinye
 
Ana hangen jerin motoci a yayin wani go slow a gadar Allahbad a kasar India
 
Jama'ar da rikici ya raba da muhallansu na ci gaba da zama a sansanin 'yan gudun hijira dage kudancin Philippines.