ZAMANTAKEWA: Kalubalen Da Ka Iya Janyo Rarrabuwar Kawunan Al'umma, Fabrairu 12, 2025

Zainab Babaji

A yau shirin Zamantakewa ya tattauna ne da masu aikin wanzadda zaman lafiya.

Rashin fahinta tsakanin al'umma da fuskoki daban-daban da suka hada da addini, ko fafutukar neman arziki ko bambancin kabila ko siyasa na daga cikin kalubalen da ya janyo rarrabuwar kawunan al'umma, da a shekarun baya suke zama tare.

Kungiyoyi masu zaman kansu na iya kokarinsu wajen aiwatar da tsare-tsare da suke da yakinin suna taimakawa wajen fahintar matsalolin da samadda hanyoyin warware su.

Saurari shirin da Zainab Babaji ta gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

Magance Kalubalen Da Ka Iya Janyo Rarrabuwar Kawunan Al'umma