Amurka ta baiwa jamhuriyar Nijar taimakon kayayyakin aiki na dala miliyan tara, domin agaza mata wajen yaki da ta'adanci.
WASHINGTON, D.C —
Gwamnatin Amurka ta baiwa Jamhuriyar Nijar taimakon kayayyakin aiki na dala miliyan tara domin taimaka mata wajen yaki da ta'adanci.
Jakadiyar Amurka a jamhuriyar Niger Eunice Reddick ce ta yi wannan bayani a wajen bikin mika wannan taimako kamar yadda wakilin sashen Hausa Chaibo Mani ya aiko da rahoto.
Amurka ta bada wannan taimako ne domin karawa kwamitin kwarin gwiwar yaki da ta'adanci.