An Kai Hari Kan Dakarun Amurka a Iraqi

Mideast Iraq Mosul US

An cilla makaman roka da dama a yankin da matsugunin dakarun kawance da Amurka ke jagoranta ke zaune a Bagadaza, babban birnin Iraqi.

Babu dai wani rahoto da ya nuna an samu jikkata a harin, wanda aka kai da safiyar yau Lahadi a yankin da ake kira Green Zone.

Yankin da aka kai harin na kusa ne da ofishin jakadancin Amurka, a cewar kakakin gamayyar dakarun.

Wannan shi ne hari na baya-baya nan cikin jerin hare-haren da ke kaikaitar wannan matsugunin dakarun hadin gwiwar.

Babu koma wanda ya dauki alhakin harin ya zuwa yanzu.

A watan da ya gataba, Amurka ta kashe Janar din kasar Iraqi mafi girma, Qassem Soleimani, a wani hari da ta kai da jirgi mara matuki a Bagadaza.

Kwanaki kadan bayan kisan, an raunata wasu dakarun Amurka bayan wani harin makami mai linzami da Iran din ta kai a Iraqi a matsayin daukar fansa.