A na sa ran gudanar da idin na karamar sallah na bana ranar Jumma'ar nan ko Asabar mai zuwa wato 21 ko 22 ga watan nan na Afrilu.
A helkwatar JIBWIS da ke Utako Abuja, Dr. Muhammad Kabir Hauruna Gombe ya rufe tafsirin da jan hankalin duk wanda Allah ya ba wa jagoranci musamman irin na dimokradiyya ya sani akwai wa'adin kammala mulkin.
Shehun malamin ya ce abun da zai taimakawa jagororin shi ne wasu shugabannin da su ka shude.
Masallacin Helkwatar JIBWIS Da Ke Utako Abuja
Hakanan malamin ya bayyana shirin JIBWIS na daukar nauyin marayu mata masu kwazon karatu a lokacin auren su.
Mai martaa Sarkin Bwari Alhaji Muhammad Musa Ijakoro ya halarci rufe tafsirin a madadin sarakunan yankin birnin tarayya Abuja.
Taron Rufe Tafsirin Al'qurani A Masallacin Helkwatar JIBWIS Da Ke Utako Abuja
An ga mutane na nuna juyayin karatowar karshen azumin da kan kasance wata da mutane kan kara kaucewa miyagun aiyuka yayin da wasu masu hannu da shuni kan kyautatawa sauran talakawa.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5
An Rufe Majalisun Tafsiri Da Dama Don Shirin Umrah Da Idin Karmar Sallah.mp3