Ana Dakon Sakamakon Zabe a Togo

Wani jami'in zabe yana kidaya kuri'u a birnin Lomé na kasar Togo, a zaben shugaban kasar da aka yi ranar 22 ga watan Fabrairu, 2020.

Al’umar Togo na dakon sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a kasar.

A jiya Asabar masu kada kuri’a suka dunguma zuwa rumfunan zabe, domin zaben wanda zai jagoranci kasar cikin shekara biyar masu zuwa.

Jaridar yanar gizo ta Atlantic Federation of African Press Agency (FAAPA) ta ruwaito cewa hukumar zaben kasar ta CENI na shirin fitar da sakamakon a gobe Litinin.

‘Yan takara bakwai ne ciki har da Shugaba mai ci Faure Gnassingbe na jam’iyyar UNIR ke takarar mukamin shugaban kasar.

Sannan akwai babban abokin hamayyarsa, Mr. Jean-Pierre Fabre na jam’iyyar adawa ta ANC a takarar.

Tun da yammacin jiya Asabar aka rufe rumfunan zabe.

Shafin yanar gizo na Al Jazeera, shi ma ya ruwaito cewa ana can ana kan kidaya kuri'un.

Wakilin Muryar Amurka Irene Houngbo, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana, ko da yake, akwai korafe-korafe a nan da can kan cewa an tafka magudi.

Masu sa ido kan ala’muran siyasar kasar ta Togo sun ce akwai alamu da ke nuna cewa Shugaba Gnassingbe ne zai lashe zaben.