Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya taya Boris Johnson murnar zama sabon Firai Ministan Birtaniya, tare da jinjinawa Theresa May wacce ta sauka a mukamin kan irin shugabanci na gari da ta yi.
Wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba shugaba Buhari shawara kan harkar yada labarai, Garba Shehu, wacce Muryar Amurka ta samu ta email, ta ce, "a Najeriya, muna mutunta zabin al’umar Birtaniya, kuma a shirye muke mu yi aiki da sabon Firai Ministan domin karfafa dangantakarmu."
Sanarwar ta kara da cewa, "Birtaniya ta kasance daya daga cikin kawayen Najeriya na kut da kut, musamman a fannin kokarin da wannan gwamnati ke yi na inganta matakan tsaro tare da dakile ayyukan cin hanci da rashawa."
Cikin sanarwar shugaba Buhari ya kara da cewa, Najeriya tza ta ci gaba da mutanta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, "ba tare da yin la’akkari da wanda yake shugabanci ba."