Rahotanni daga Kamaru na cewa, jami'an tsaron kasar sun kamu wasu 'yan Najeriya 30 da suka shiga yankin kasar, mafi aksarinsu mata da yara kanana.
Jami’an tsaron sun ce tsare sun mutanan ne a wata mota kirar bas, a lokacin da ta ketara zuwa cikin iyakar kasar a ranar Asabar din da ta gabata.
Sun ce mutanen, sun fito ne daga yankin Gamborou Ngala, wani yankin da ya taba fadawa karkashin ikon kungiyar ta Boko Haram.
Shugaban rundunar ‘yan sandan yankin Arewa mai nisa a kasar ta Kamaru, Shettima malla Abba, ya ce a lokacin da aka tsare motar da ke dauke da ‘yan Najeriyan, sun ga wasu alamu tattare da mutanen da suka dasa shakku a zukatansu.
“Mun tsare mutanen ne, saboda sun gaza nuna wata shaidar iznin shiga kasar, sannan sun kasa ba da sunayen mutanen da suka ce za su kai wa ziyarar a kasar ta Kamaru, sannan sun fito ne daga yankin da ‘yan Boko Haram ke da tasiri.” Inji Shettima
Dalilin Kama Mutanen
Sai dai jami’in ‘yan sandan, bai ba da wata shaida da ke nuna cewa ‘yan Najeriyar, na da alaka da kungiyar ta Boko Haram ba, amma ya ce, ba sa sako-sako da irin wannan batu.
Ya kara da cewa, a baya, ‘yan kungiyar ta Boko Haram, sukan bat da kama a matsayin fasinjoji, ko ‘yan kasuwa ko kuma malamai, inda sukan kai hare-hare a kasar ta Kamaru, sannan dadin-dadawa, kungiyar kan yi amfani da ‘yan mata ne wajen kai hare-hare.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin Najeriya ba su ce uffan ba, dangane da tsare mutanen ba.
Gwamnan Arewa mai nisa a kasar ta Kamaru, Midjinyawa Bakari, ya ce hare-haren Boko Haram sun ragu matuka a ‘yan watannin nan, saboda irin tsauraran matakan tsaro da suke dauka.
Amma ya yi gargadin cewa, ‘ya’yan kungiyar, kan yi amfani da duk irin damar da suka samu, musamman a lokutan da mutane ke tafiye-tafiye domin halartan bukuwa na addini ko kuma a lokutan hutu.
“Na umurci ‘yan sanda da sojoji, da su tsaurara matakan tsaro aknan iyakar kasar, a daidai lokacin da al’umar kasar ta Kamaru ke shirin fara ayyuka na addini, kamar lokacin watan azumi da za a fara a ranar biyar ga watan Mayu, da kuma ranar ma’aikata ta duniya da za a yi a ranar daya ga watan na Mayu, da kuma bikin da za a yi na kasa a ranar 20 ga watan Mayu, ‘yan kungiyar ta Boko Haram, kan yi amfani da wadannan lokuta domin kai hare-harensu a masallatai da kasuwanni.” Inji Midjinyawa Bakari.
Har ila yau, gwamnan na Arewa mai nisa, ya dangana karuwar samun zaman lafiyan da aka gani, ga irin ayyukan da dakarun hadin gwiwa na kasashen Kamaru, Chadi, Nijar da Najeriya ke yi a yankin Tafkin Chadi.
Shigar ‘Yan Boko Haram Kasar Kamaru
Tun shekaru shida da suka gabata, kungiyar Boko Haram ta tsallaka cikin Kamaru daga Najeriya, inda ta rika kai hare-hare, bayan da dakarun Kamarun suka fara taimakawa takwarorin aikinsu na Najeriya wajen yaki da ayyukan ta’addanci.
Hukumomin kasar sun ce, akalla ‘yan kasar Kamaru 1,500 suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren kungiyar.
Najeriya tare da hadin gwiwar wasu dakarun ketare, sun yi nasarar kwato mafi aksarin yankunan da suka fada karkashin ikon kungiyar ta Boko Haram, lamarin da ya sa aka samu saukin hare-harenta.
Amma a ‘yan watannin baya, kungiyar ta kara zafafa hare-harenta a yankunan arewa maso gabashin Najeriyar.