Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya sake komawa Isra’ila, inda zai sake neman a kara tsawaita yarjejeniyar dakatar da bude wuta saboda a sake fadada damar sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza a kuma kara shigar da kayayyakin agaji cikin yankin.
Hakan na faruwa ne bayan da Blinken ya kara jaddada goyon bayan Amurka ga Ukraine yayin da hukumomin kasar ke shirin fafatawa a daidai lokacin da aka tunkari yanayi na hunturu.
Your browser doesn’t support HTML5
DUNIYAR AMURKA: Amurka Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Ukraine Duk Da Rikicin Isra’ila Da Hamas - 5'45"