Gasar Zakarun Turai: Real Madrid Ta Kai Zagayen Quarter-Final

'Yan wasan Real Madrid na murnar kai wa zagayen Quater-final (Photo by Thomas COEX / AFP)

Arsenal, Aston Villa, da Borussia Dortmund duk sun samu nasarar zuwa matakin quarter final.

Real Madrid ta doke Atletico Madrid a bugun fenariti a gasar Zakarun Turai ta Champions League don ci gaba da kare kambunta a ranar Laraba tare da samun tikitin shiga wasan quarter-final.

Dan wasan baya Antonio Rüdiger ne ya zura bugun fenariti na karshe wanda ya tabbatar da nasarar 4-2 bayan ‘yan wasan Atletico biyu sun kasa cin nasu.

Arsenal, Aston Villa, da Borussia Dortmund duk sun samu nasarar zuwa matakin quarter-final.

Atletico ta yi nasarar 1-0 bayan mintuna 90 a filinta na Metropolitano, wanda ya kawar da rinjayen Madrid na 2-1 daga wasan farko.

Tauraron Madrid, Vinícius Júnior, ya buga fenariti da ta tashi saman ragar Atletico.

Dan wasan Atletico, Conor Gallagher, ne ya fara jefa kwallo tun farkon wasan