Yau Alhamis aka shiga yini na biyu na zaman makoki da hukumomin Mozambique suka ayyana, bayan da wata mummunar guguwa dauke da ruwan sama ta halaka daruruwan mutane a wasu kasashen da ke kudancin Afirka.
Guguwar wacce aka wa lakabi da “Idai” ta yi tafiyar kilomita 170 cikin sa’a guda, inda ta fada akan birnin Beira na kasar ta Mozambique mai tashar jiragen ruwa a makon da ya gabata, kafin daga nan ta nausa zuwa kasashen Zimbabwe da Malawi
Shugaban Mozambique Filipe Nyusi, ya ce mutum 200 aka tabbatar da mutuwarsu, amma bayan wani rangadin kasar da ya yi ta jirgin sama, ya ce adadin wadanda suka mutun zai iya kai wa dubu daya.
A Zimbabwe ma, an samu mutane da dama da suka mutu, kamar yadda wannan jami’in ba da agajin gaggawa na kungiyar Red Cross ya tabbatar
“Ya zuwa yau, mun samu tabbacin mutuwar kusan mutum 100, sannan ba a ga kusan mutum 200 ba.”