Majalisar ministocn gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kudiri aniyar karrama mata ta wajen basu guraben a zabe. Hakan ya biyo bayan kokawar da ko yaushe mata ke yi na maida su cikin cudanyar mulki, da rike mukamai. Musamman kasancewa suna ganin sune kan gaba a harkokin siyasa.
Matan sun koka ta yadda ake amfani dasu a wajen siyasa, da yakin neman zabe da sauran abubuwan da suka shafi siyasa, amma basu da gurbi mai yawa.
A kudirin gwamnati ta mika ma majalisar dokoki karin guraben mukamai na zabe daga kashi 15 zuwa 25, da kuma na nadin mukamai daga kashi 25 zuwa 30.