Wasu nakiyoyi da wata 'yar kunar bakin wake ta tayar a wata kasuwa a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, sun kashe akalla mutane 14.
Shaidun gani da ido suka ce akalla mutane 50 ne suka jikkata.
Jami'ai a jihar suka ce fashewar ta auku ne da safiyar lahadin nan a kofa shigar kasuwar dake Damaturu babban binrin jihar Yobe.
Babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin. A farkon wannan wata akalla mutane 9 ne suka halaka lokacinda wata 'yar harin kunar bakin wake ta auna masu masu sallar idi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
harin bam a Damaturu
Ahalinda ake ciki kuma wani bam da aka boye cikin wata mota ya tashi a harabar wani O'tel a Mugadishu a ranar lahadin nan, ya kashe akalla mutane 13.
A cikin O'tel din ne kuma ofisoshin jakadancin kasashen China da Masar suke.
Kungiyar mayakan sakai ta al-shabab ta dauki alhakin kai wannan hari.