Rundunar 'Yan-sandan jahar Kaduna ta ce ta kama wasu daga cikin tsagerun da ake zargi da hannu wajen kashe 'yan-sanda hudu a kwanakin baya, sannan kuma ta kama wasu barayin mutane da motoci da sauran masu aikin assha a jahar.
WASHINGTON DC —
Mukaddashin kwamishinan 'yan-sandan jahar wanda kuma shine mataimakin kwamishina mai kula da kudi, DC Magaji Ahmed Kontagora ne ya yiwa manema labaru karin haske a Kaduna.
Ranar goma sha daya ga wannan wata na Augusta ne wasu yan-bindiga su ka tare 'yan-sanda a yankin Jarkasa dake garin Rigasa, inda bayan sun yi misayar wuta na wani dogon lokaci aka kashe 'yan-sanda guda hudu wanda tun daga nan rundunar 'yan- sandan ke ta fafutukar ganin ta farke layar masu wannan barna.
Saurari rahoton Isa Lawal Ikara
Your browser doesn’t support HTML5
Rundunar Yan Sandan Jihar Kaduna Ta yi Zagayen Yan Ta'adan Da Suka Kashe Yan Sanda Hudu 3'34