Labaran Wassanin VOA Hausa na ran 23 ga watan Yuni, 2014, Kofin Duniya, Ghana
Aliyu Mustapha
John Boye, Ghana
Shirin zai duba matsayin dukkan kasashe bayan wassani bibbiyu, zargin cuku-cuku a Ghana da kuma ‘yan wasan da kasashen suka dogara a kansu kacokan.
WASHINGTON, DC —
A yanzu dai kowace kasa ta buga wassani bibbiyu a gasar Cin Kofin Duniya da ake gudanarwa a Brazil, saboda haka yanzu kowacce ta san matsayinta. Wasu sun zarce, wasu kuma ana harramar komawa gida. Yayinda wannan ke faruwa kuma, a Ghana wata sabuwa ta bullo bayanda aka bankado cewa wasu jami’an hukumar kwallo ta GFA sun nemi toshiyar baki don su rinka barin ana cin Ghana a kwallon da take bugawa da wasu kasashe. Bayan wannan,zamuji ra’ayoyin wasu akan ko wadanne ‘yan wasa ne da, in babu su, zai yi wa kasashensu wuyar cin kwallo?