A shirin Lafiya na wannan makon mun yi magana ne a kan yoyon fitsari da ya zama daya daga cikin matsalolin kiwon lafiya da ke shafar mata musamman wadanda suka fuskanci matsala a lokacin haihuwa.
Me ke janyo Fistula, wato yoyon fitsari ga mata?
A kokarin da ake yi na ganin cewa an shawo kan wannan matsala Gidauniyar Bashir Fistula Foundation tare da hadin gwiwar Babban Asibitin Gwarimpa da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren sun bullo da wani tsari na yiwa mata masu fama da wannan matsalar aikin gyara kyauta.
Yin aikin tiyata ga mata masu yoyon fitsari bayan haihuwa
Saurari cikakken shirin da Hauwa Umar ta gabatar:
Your browser doesn’t support HTML5
LAFIYA UWAR JIKI: Batun Matsalar Yoyon Fitsari Ga Mata Bayan Haihuwa, Janairu 30, 2025.mp3