Da yammacin jiya Juma’a ne Majalisar dattawan Amurka ta amince da kudirin kashe kudin gwamnatin, lamarin da ya dakile rufe wani bangaren gwamnatin kana ya shawo kan adawar Democrat ga matakin.
Kudirin ya samu amincewar mutane 54 a kan wasu 46 masu adawa bayan shawo kan kalubalen dake hana mahawara kan matakin, wanda ke bukatar akalla kuru’u 60.
Majalisar wakilai mai rinjayin Republican ta amince da kudirin tun farkon wannan mako domin cimma wa’adin dake karewa cikin daren ranar Juma’a ta yanda gwamnatin zata ci gaba da gudana.
'Yan Democrats a majalisar dattijai sun yi sabani da juna kan ko za su goyi bayan kudurin ci gaba da gudanar da gwamnati na gajeren lokaci, wanda zai ba gwamnatin damar kashe kudade na watanni shida masu zuwa, kana ya rage yawan kudaden da gwamnati ta kashe da kusan dala biliyan 7 a shekarar da ta gabata, da karkatar da kudade ga sojoji da kuma nesantar kashe kudaden da ba na tsaro ba.
Yawancin 'yan jam'iyyar Democrat sun bayyana fushinsu bayan da jagoran Democrat a zauren majalisar, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai Chuck Schumer, ya ba da sanarwar a daren ranar Alhamis cewa duk da bai amince da kudirin ba, matakin rufewa zai kasance "zabi mafi muni."
Da yake magana a zauren majalisar dattijai da safiyar Juma’a, Schumer ya ce rashin tabbatar da kudirin kashe kudaden gwamnati na Republican zai ba da karin iko ga hukumar DOGE mai kokarin inganta Ma’aikatun Gwamnati da Elon Musk ke jagoranta, ciki har da rufe wasu hukumomi.