Mata Ma'aikata Za Su Dena Biyan Kudin Mota a India

Waso motocin sufuri na bas a India

Hukumomin New Delhi a India, sun kaddamar da wani shirin da zai rika safarar mata zuwa wuraren ayyukansu kyauta a bas-bas, shirin da Ministan birnin ya kwatanta shi a matsayin “mai cike da tarihi” wanda kuma zai kare lafiyar mata da ke fita aiki.

India dai na daya daga cikin kasashen da mata ba su cika fita aiki ba a duniya, yayin da cin zarafin da ake musu ke karuwa a kasar, wacce ita ce ta biyu a jerin kasashe mafiya yawan jama’a a duniya.

An kaddamar da shirin na safarar mata kyauta zuwa wuraren ayyukansun ne a jiya Talata, inda aka rika ba su wani tikiti na musamman mai launin hoda.

Fyaden da wani gungun mutane ya yi wa wata daliba a cikin bas har ta rasa ranta a shekarar 2012, ya sa kasashen duniya sun sawa kasar ta India ido, lamarin da har ya haifar da mummunar zanga zanga.