Mike Pence Ya Jinjinawa 'Yan Sama Jannatin Farko a Duniya

A wannan hoto da aka dauka a jihar a Florida, a ranar 16 ga watan Yulin, 1969. Neil Armstrong yana yin ban kwana da jama'a yayin da suke shirin jirign da zai kai su duniyar wata

Gwamnatin ta Trump ta kaddamar da wani shiri na sake komawa duniyar ta wata a shekarar 2024 da nufin sauka a duniyar Mars a karon farko nan da shekarar 2033.

Yayin da ake bikin cika shekaru 50 da a karon farko bil Adama ya saka kafarsa duniyar wata, Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, ya jinjinawa Amurkawa nan uku ‘yan sama jannati da suka taimaka wajen kai wannan ziyarar ta farko a duniyar watan.

A cewar Pence, abin da suka yi, ya wuce lashe rigerigen da duniya ke yi na zuwa Duniyar watan, domin sun taimaka wajen had akan Amurkawa, sannan a karon farko, daukacin mutanen duniya sun dukule wuri guda.

A ranar 20 ga watan Yulin 1969, jirgin sama jannatin Amurka mai suna “Eagle” ya sauka, inda dan sama jannatin nan marigayi Armstrong ya saka kafarsa a karon farko a Duniyar wata.

Wannan nasara ta zuwa duniyar wata, ta kara daraja Amurka a idon duniya, musamman ma lura da cewa a lokacin ana yakin cacar baka da Tarayyar Soviet wacce ita ma ta zamanto kasa ta farko da ta dasa tauraron dan adam a duniyar watan.

A yau Asabar shugaban Amurka Donald Trump, ya fada a wata sanarwa cewa, kai wa ga duniyar watan, wani mataki ne na sharar fagen wasu aikace-aikace na zuwa za a yi nan gaba a duniyar ta wata.

Gwamnatin ta Trump ta kaddamar da wani shiri na sake komawa duniyar ta wata a shekarar 2024 da nufin sauka a duniyar Mars a karon farko nan da shekarar 2033.