Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Kanal Hamid Ali, mai ritaya ne ya anbata haka a wata hira da yayi da muryar Amurka.
Yace, gwamnati ce yakamata ta samarwa Sojoji makamai, domin fuskantar kalubalen dake cima Najeriya, tuwo a kwarya.
Ya kara da cewa akwai siyasa, a lamari, domin a cewarsa idan hara gwamnati na son magance lamarin tuni da tayi haka, Idan ko bata da niyyar murkushewa haka za’a ci gaba.