Da misalin karfe 12 daren ranar Litinin, sabbin matakan da hukumomin Najeriya suka saka don kare yaduwar cutar COVID-19 suka fara aiki.
WASHINGTON D.C. — 
Kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar ne ya bayyana sabbin matakan yayin wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin Najeriya.
Muktar Mohammed, daya daga cikin manyan jami’an gudanarwa a kwamitin ya ce:
- Tarukan Bukukuwa kamar na aure, kada su wuce mutum 50, kuma an fi so a yi a budadden wuri.
 - Ya zama dole mahalarta tarukan su saka takunkumin rufe baki da hanci.
 - Wajibi ne a rika tsabtace hannaye.
 - Wajibi ne kuma bada tazara.
 
Fannin Sufuri
- Ba a kayyade tafiye-tafiye a tsakanin jihohi ba.
 - Amma ana so masu harkar sufuri su bi ka’idojin da ma’aikatar sufuri ta gindaya, a kuma tabbatar an yi amfani da matakan kariya – a kuma tabbatar da an ba da tazara a inda ya kamata.
 
Ma’aikatun Gwamnati
- Muna ba da kwarin gwiwar da a ci gaba da aiki daga gida musamman daga ma’aikatan da suke kasa da mataki na 12
 - Wadanda suke mukamin aiki na 12, za su iya komawa ofis.