A cikin 'yan kwanakin nan, Obama ya karbi korafe-korafe daga shugabannin majalisa, gwamnonin jam’iyyar Democrat da kuma manyan masu ba da taimako da mika ra'ayinsu game da makomar yakin neman zaben Biden sakamakon mummunar muhawarar da ya yi a ranar 27 ga Yuni da Donald Trump.
Joe Biden
Duk da ya saurari wadannan kuken, Obama ya dage cewa Biden ne yake da hurumin ya yanke shawarar ci gaba da kasancewa a takarar, a cewar mutane da yawa da suke da masaniya kan lamarin, wadanda suka nemi a sakaya sunayensu.
Wannan wani lokaci ne da Obama ke bukatar ya samar da daidaito a matsayinsa na dattijo a jam’iyyar kan yadda zai magance korafin wadanda suka kai masa korafi ba tare da ya ci dunduniyar tsohon mataimakinsa ba.
-AP