Za A Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin Bana Ran 14 Ga Watan Gobe
Ibrahim Garba
Alhazai a Makka Zagaye Da Ka'aba
Hukumar Alhazan Nijeriya ta bayyana cewa ran 14 ga watan Satumban nan za a fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana.
WASHINGTON, DC —
Bayan wata ganawa da Kamfanonin jiragen sama, Hukumar Alhazai ta Nijeriya ta bayyana cewa ranar 14 ga watan gobe ne za a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, a cewar wakilinmu a Abuja Saleh Shehu Ashaka.
Shugaban Hukumar Alhazan Alhaji Muhammad Musa Bello, wanda ya sanar da ranar fara jigilar, ya ce hakkin kowani kamfanin jiragen sama ne ya tabbatar cewa kowace fasinja maniyyaciya na da muharrami.
Da ya ke nasa bayanin, jami'in yada labaran MaxAir, wato kamfani mai kaso mafi tsoka na fasinja maniyyatan, Ibahim Dahiru ya ce tuni su ka dau ma'aikatan tantancewa da tabbatar da cewa an bi ka'ida. To amma ya ce su ma hukumomin alhazai nauyin hakan ya rataya a wuyansu.
Your browser doesn’t support HTML5
Za A Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin Bana Ran 14 Ga Watan Gobe - 1:57