Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta yi barazanar korar wani mambanta da ya shigar da kara a kotu, yana neman Shugaba Muhammad Buhari ya yi tazarce.
Charles Enya, mamba a jam'iyyar ta APC a jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya, ya garzaya kotu, yana neman a bari Shugaba Buhari da sauran gwamnoni su nemi wa’adi na uku.
Sai dai wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar, Malam Lanre Issa Onilu ya fitar a jiya Alhamis kamar yadda rahotanni suka nuna, ta kwatanta masu neman Shugaba Buhari ya yi tazarce a matsayin “yan kanzagi.”
Sanarwar ta kara da cewa, masu kambama wannan batu, ba wasu ba ne illa “sojojin haya,” da ke son su “ta da zaune tsaye” tare da yi wa tsarin dimokradiyya “zagon kasa.”
Buhari, mai shekaru 76, wanda aka sake rantsarwar a wa'adi na biyu a watan Maris, ya fito ya yi watsi da wannan batu, yana mai cewa ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
A cewar Onilu, an fitar da wannan sanarwa ce, musamman don ta zama garagadi ga Enya.
“Da farko mun yanke shawarar mu yi watsi da shi, amma, mun ga ya kamata mu aika mai da sako karara da sauran masu son ta da zaune tsaye,” sanarwar ta ce.
Ya kara da cewa, “mun yi kokari mu binciki sahihancin ikrarin da yake na cewa shi mamba ne a jam’iyyarmu, idan hakan ne, za mu sa reshen jam’iyyarmu da ke mazabar da ya fito ya kore shi.”