Wakiliyar Sashen Hausa daga Damagaran Tamar Abari ta aiko da rahoton cewa yankin Damagaran basu fito wurin zaben ba kamar yadda suka fito a zagayen farko. A cikin rahoton ga abinda take cewa.
WASHINGTON, D.C. —
A da-dai karfe 8 na safe aka bude yawancin runfunar zaben babu cunkoson jamaa, kuma an fara zabe ba tare da matsala ba kamar yadda wani shugaban mazaba ke cewa.
A lokacin da tafi runfar zabe na farko mai lamba 4 tace mutane basu wuce mutane biyu zuwa ukku ba.
Ga abinda malamin zaben mai suna Muntari Lawal ya shaida wa Tamar din.
‘’Mun bude runfar zabe karfe 8 dai-dai, kuma kayan aiki an kawo kome da kome sai wani takarda da ake cewa kashe, wato tawadar da ake sawa mai jefa kuria bayan y agama jefa kuuriaar sa.
Da Tamar ta tambaye shi ko yaya ma’aikatan su?sai yace duka su biyar kowa nan bakin aikin sa.