A cikin shirin na wannan makon a Jamhuriyyar Nijar daliban kasar sun kammala taron shekara-shekara na tunawa da abokan karantunsu uku da jami’an tsaron kasar suka kashe a shekarar 1990, da wasu rahotanni
A cikin na wannan makon Mminwara wasa ne na al'adun gargajiya na mutane a karamar hukumar Shani ta jihar Borno a arewa maso gabashin Njeriya, inda kabilu daban daban suke haduwa domin baje kolin al'adunsu, da wasu rahotanni
A karshen wannan watan na Fabrairu ne ake sa ran za a yi babban taron jam`iyyar inda za ta zabi shugabanninta na kasa.
A Najeriya batun cunkoso a gidajen gyara hali ya jima yana daukar hankalin jama'a kuma duk da kokarin da mahukunta ke yi don magance matsalar har yanzu ana samun cinkoso.
Matasan da hukumar yaki da safara da fataucin bil’adama ta Najeriya NAPTIP ta ceto daga hannun masu safarar mutane yayin kokarin tsallakawa da su kasar Libya, sun bayyana nadama tare da yin gargadi ga ‘yan uwansu matasa.
A Somaliya mutanen da ke tserewa fari na kwarara zuwa sansanonin da ke wajen birnin Mogadishu, don sun rasa abinci, da ruwan sha da matsuguni. Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanayin fari ya sanya kimanin mutane miliyan 13 fuskantar matsananciyar wuya.
Wata kungiyar fafutuka ta TLP ta kudiri aniyar gudanar da taron gangami a ranar Juma’a a birnin Yamai da nufin ta da mahukunta daga barci akan matsalolin tsaro da wasu batutuwa.
Kungiyar tarayyar Afirka ta kammala taron ta na kwanaki biyu a hedikwatar birnin Addis Ababa dake kasar Ethiopia, tare da yanke muhimman shawarwari.
Shugaban kula da dokokin ma'aikatar man fetur ta Najeriya, Malam Faruk Ahmed, ya yi cikakken bayani a game da akasi da aka samu a game da gurbataccen man fetur a wasu sassan kasar.
Akalla mutum shida ne suka mutu a sakamakon wasu hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihar Nejan dake Arewacin Najeriya.
Rahotanni daga hukumomi a Jihar Bauchi na bayanin cewa kwamitin tsaro da suka hada har da jami’an tsaro, suna tsare wasu mutane bisa zargin sayar da katin yin alluran rigakafin coronavirus.
Jama'a da yawa da ma dillalan shanu a jihar Abia na ci gaba da yin tsokaci akan batun rufe babbar kasuwar shanu da mahautar garin Aba, da ke Najeriya da gwamnatin jihar ta yi.
Wasu masu bincike a Afirka, suna kirkirar fasahar amfani da murya wadda zata habbaka harsunan asali a Nahiyar, da wasu rahotanni.
Kungiyoyin matasa magoya bayan jam’iyyar APC sun juya taron rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihohi zuwa dandalin kamfen din amsar madafun ikon jam’iyyar.
Wani rahoton cibiyar bincike ta International Budget Partenership ya gano rashin haske wajen tafiyar da kudaden da aka yi tanadi domin yaki da anobar COVID-19a kasashe da dama
Rikice rikicen siyasa na ci gaba da daukar hankalin jama'ar Najeriya daidai lokacin da lokutan gudanar da zabubuka ke kara matsowa.
Fitattun sojojin Amurka sun kashe shugaban kungiyar IS, a wani samame da suka kai cikin dare a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin Syria, in ji shugaban kasar Joe Biden.
A yayin da wa’adin da gwamnatin jamhuriyar Nijar ta dibarwa wasu ‘yan Rwanda don ficewa daga kasar ke cika ranar Alhamis 3 ga watan Fabrairu, lauyar da ke kare su ta bayyana damuwa.
Domin Kari