Hugo Maradona, kanin Diego Maradona kuma tsohon dan wasan kwallon kafa ya rasu. Ya rasu yana da shekaru 52.
‘Yan Najeriya sun mayar da martani game da kalaman Ministan Shari’ar kasar Abubakar Malami na cewa gwamnatin tarayya na amfani da kudaden da aka kwato a kasashen waje wajen gudanar da manyan ayyuka na ciyar da kasar gaba.
Hauhawar farashin dalar Amurka na ci gaba da kawo babban cikas ga ‘yan kasuwar a Najeriya musamman wadanda ke fitar da kaya zuwa kasashen duniya.
Yayin da kiristoci a Najeria suka shiryawa shagulgulan Kirsimeti, wasu ‘yan kasar sun koka da matsin tattalin arziki dake kasar, da wasu sauran rahotanni
A cikin na wannan makon ma'aikatar gandun daji ta kasar Nijar ta bai wa wasu mazauna yankunan karkara a karkashin kungiyoyinsu, horo domin sanin hanyoyin bi na samun tallafin gudanar da ayyukan dogaro da kai, da wasu rahotanni
A jamhuriyar Nijer kungiyar AJSEM da hadin guiwar UNESCO sun shirya wani taro domin fadakar ‘yan jarida akan bukatar mutunta ‘yancin ‘yan cirani ta yadda za a daina amfani da kalaman da ke kama da na cin zarafin bakin haure a yayin bada labari
Wata kungiyar kare hakkin bil'adama wato Human Rights Watch ta kasa da kasa yau Alhanis, ta zargi mayakan 'yan awaren yankin Anglophone na kasar Kamaru dakaiwa makarantu da dalibai da malamai hari a lokacin yakin basasa da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.
A jamhuriyar Nijar shugabannin al’umar karkarar Lahari dake yankin Diffa sun bayyana damuwa dangane da yanayin da ayyukan hakar man fetur suka jefa su ciki inda gurbacewar muhalli ta shafi ayyukan noma da kiwo, saboda haka suka bukaci hukumomin kasar su dubi wannan al’amari kafin abin ya tsananta.
A Najeriya nasarorin da kungiyoyin fafutukar kare hakkin yara ke samu na haduwa da cikas domin wasu na yi masu zagon kasa, sai dai kuma kungiyoyin da hukumomin kare hakkin bil'adama sun ce sai sun ga abinda zai turewa buzu nadi.
A jamhuriyar Nijar hukumomin kiwon lafiya sun bada sanarwar dakatar da tallafin kudaden tiyatar haifuwa da aka saba yiwa mata kyauta sakamakon wasu dalilai masu nasaba da tsarin aikin, amma kuma za a ci gaba da tsarin bada magani kyauta ga mata masu juna biyu da yara kanana.
‘Yan bindiga sun kashe shugaban kwamitin kananan hukumomi da raya karkara na majalisar dokokin jihar Kaduna, Rilwanu Aminu Gadagau mai wakiltar mazabar Giwa ta yamma.
A Najeriya bisa ga yadda lamarin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a yankin Arewa da kuma kasawar gwamnatin kasar wajen magance matsalar ya sa gamayyar kungiyoyin Arewa ta dora alhakin faruwar matsalolin kan gwamnatin kasar.
Rikicin cikin gida a Jam’iyar APC, na kara ta’azzara inda bincike ke bayyana akwai Jihohi sama da goma da rikicin ya shafa.
Gwamnan Jihar Tahoua ya kai ziyara a babban asibitin birnin Jaha, domin gaida sojojin jamhuriyar Nijar da wadansu mahara da a ke zaton sun tsallako ne daga kasar Mali su ka jikkata a yankin Tilliya, a wani kazamin arangama.
A jamhuriyar Nijar wasu ‘yan majalisar dokokin kasar sun zargi kakakin majalisar Alhaji Seini Oumarou da taka doka sakamakon rashin ba su damar sauraren Ministan tsaro da takwaransa na cikin gida a game da abubuwan da suka faru a ranar 27 ga watan Nuwamba da ya gabata a garin Tera.
A shirye shiryen fara amfani da sabuwar fasahar 5G a Najeriya, a jiya ne kamfanonin sadarwar wayar salula biyu wadanda suka hada da MTN da MAFAB suka yi nasarar samun gwanjon lasisin fasahar.
Hukumar yaki da cin hanci a Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani aikin zuba ido akan ayyukan ‘yan sandan kula da zirga-zirga da nufin tantance zahirin abubuwa irin na cin hanci da ake zargin su da aikatawa.
A cikin shirin na wannan makon bayan wasu kwanaki da kai hari a wani gidan yari a jihar Filato a Najeriya, iyalin ma’aikacin gidan yarin da ya rasa ransa a lamarin, sun bukaci gwamnati da ta taimaka musu, da wasu rahotanni
Domin Kari