Hukumomin Nijar sun ayyana rana Talata a zaman ranar hutu a fadin kasar, bayan kwashe daren jiya na 27 na azumin watan Ramadan, domin dacewa da daren Lailatul Kadir, inda a ka kwana ana yi wa kasar da askarawan ta addu'o'in samun zaman lafiya.
Hukumar sadarwar jamhuriyar Nijar, ta kudiri aniyar samar da karin kudaden tallafi ga kafafe yada labarai masu zaman kansu kamar yadda abin yake a wasu kasashen yammacin Afrika ta yadda za su kara inganta ayyukan watsa labarai da tsara shirye-shiryen ci gaban kasa.
Wasu ’yan jam’yyar PDP a jihar Adamawa sun gudanar da zanga-zangar lumana domin numa rashin jin dadinsu akan yadda hukumar zaben jihar ta ayyana Saneta Aishatu Dahiru Ahmed Binani a matsayin wadda ta yi nasara a zaben gomna a jihar Adamawa.
Hukumar zaben Najeriya INEC ta mika batun binciken kwamishinan ta na zabe a jihar Adamawa Barista Ari Hudu ga babban sufeton ‘yan sanda Baba Usman Alkali don daukar matakin doka da ya dace.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bukaci babban sufeto janar na ‘yan sandan kasar Alkali Usman Baba daya gaggauta kama tare da gurfanar da dakatatten kwamishinan zaben jihar Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari.
A lokacin da alaka ta fahimta tsakanin mabiya addinai a Najeriya ke kara tabarbarewa, wani bawan Allah kirista, 'Kabilar Igbo ya kai gudummawar butoci ga makwabtansa musulmi domin su samu saukin yin ibada a wata mai Alfarma na Ramadan, da wasu rahotanni
Ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta tabbatar da labarin kama wasu ' yan kasar a Saudiya dake dauke da miyagun kwayoyi. Sai dai kawo yanzu ba a yanke musu hukunci ba kuma ba a san makomar su ba a cewar hukumomi.
Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu, da Dokta Ngozi Okonjo-Iweala, babbar darakta a Cibiyar kasuwanci ta duniya, sun shiga jerin mutane 100 da suka fi tasiri a duniya na shekarar 2023 da Mujallar Time ta fitar.
Yau shekaru tara kenan da ‘yan ta'addan Boko Haram suka sace dalibai mata su 276 daga makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno, kuma har yanzu ba a san inda ‘yan mata 98 su ke ba.
Masu zabe a Najeriya sun nuna azamar fita runfunan zabe gobe Asabar domin kammala zabubukan da ba'a kammala ba a wadansu jihohin kasar.
Al’ummomin dake Garin Ibbi ta karamar hukumar Mashegu a jihar Nejan Najeriya da wasu kauyukan da ke kusa dasu na cikin wani yanayi na tashin hankali tare da zaman makoki bayan da wasu ‘yan bindiga suka halaka wasu mutanen yankin, suka kuma yi garkuwa da wasu.
Kamar sauren Kiristoci na sassa daban-daban na Duniya, Kiristoci a Jamhuriyyar Nijar sun gudanar da bakukuwan ranar Easter ko ranar tunawa da mutuwar Yesu Al-Masihu da tashinsa.
Kasar Faransa ta gargadi ‘yan kasar ta su guji yawo a cikin kasashen Yankin Sahel da daina zuwa yawon bude ido a cikin wadanan kasashen don gudun sace su ko kuma a kashe su, biyo bayan karuwar aika-aikar ‘yan ta'adda a kan ‘yan kasar Faransa.
Bisa ga yadda matsalolin rashin tsaro ke ci gaba da zama abin damuwa tsakanin ‘yan Najeriya, wani abu da ke kara daga hankalin jama'a shi ne yadda ‘yan bindiga ke kashe wadanda suka yi garkuwa da su bayan kuma sun karbi kudin fansa.
Hukumomin Jamhuriyar Nijar da hadin guiwar kamfanin SONIMA sun kaddamar da ayyukan rajistar kananan bindigogin da ke hannun jama’a da nufin tantance fararen hular da suka mallaki makamai don takaita hadarin da ke tattare da rike bindiga ba akan ka’ida ba.
Rikici tsakanin Fulani da Tiv na jihohin Taraba da Benue a Najeriya ya ketare iyaka zuwa Kamaru inda mazauna iyakar suke fama da hare-haren ‘yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.
A jawabin sakon Ista da ya karfafa batun bege, ranar Lahadi Fafaroma Francis ya yi addu'o'i ga al'ummar Ukraine da Rasha, ya kuma yaba wa kasashen da suka karbi 'yan gudun hijira.
Domin Kari