Hedkwatar rundunar tsaron Najeriya ta yi karin haske kan hoton da wasu ke ta sake yadawa a shafukan sada zumunta na shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa, dauke da wata bindigar soji kirar AK47, inda wasu sojoji ke gwada mai yadda ake harbawa a cikin wani Daji.
Yanzu ana samun karuwar masu sana’o’i a Amurka dake amfani da jirage marasa matuka wajen kai wa mutane biskit da shayin gahwa har kofar gidajensu, da wasu rahotanni
Ganin yadda 'yan siyasa su ka gudanar da yakin neman zabe da kuma sanya addini da malamai su ka yi, ya sa hukumar wanzar da zaman lafiya ta jihar Kaduna kiran wani taron gaggawa, inda ta ja hankalin al'uma da su guji ta da hankali a lokaci da bayan zaben gwamnoni.
Sakataren harakokin wajen Amurka Antony Blinken da ke ziyarar wuni biyu a jamhuriyar Nijar ya sanar da karin kudaden tallafi ga kasashen yammaci da tsakiyar Afrika wadanda za'a yi amfani da su don inganta rayuwar al’umomin wadannan kasashe.
A duk lokacin aka buga gangar siyasa a Najeriya, gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu suke fara hada karfi da karfe wajen wayar da kan matasa da kuma yi musu gargadi da kada su bari ayi amfani da su wajen tayar da tarzoma a lokacin zabe, tare da yin nuni da irin illolin da ke tattare da hakan.
Yayin da ake daf da gudanar da zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi a Najeriya, jama’a na kara nuna damuwa kan sha’anin tsaro a lokacin zaben.
LAFIYA UWAR JIKI: Shafe-shafen Mayukan Sauya Kalar Fata “Bleaching” Da Illolinsu, Maris 16, 2023
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Jamhuriyar Nijar a yau Alhamis 16 ga watan Maris inda zai tattauna da takwaransa Hassoumi Massaoudou ( Hasumi Masa’udu) kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu masu dadaddiyar huldar diflomasiya.
Hukumar zaben Najeriya INEC ta ba da kwarin gwiwar shawo kan dukkan matsalolin da ta samu da aiki da na’urar tantance masu kada kuri’a BVAS a ranar Asabar din nan yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha.
A wani mataki na tunkarar ta'addanci a yankin Tafkin Chadi ta dukkannin bangarori, rundunar kawancen yankin wato MNJTF ta matsa kaimi wajen afkawa ba kadai kan ‘yan ta'addan ba, har da karin samame akan fararen hular da ke taimakon ‘yan ta'addan wajen samar masu da kayayyaki ko bayanai.
A cikin shirin na wannan makon, mun duba batun sake karfafa bukatar farfado da ginshikan kyawawan dabi'u na al'ummar arewacin Najeriya daga kaka da kakanni.
Kasashen Malawi da Mozambik na kokarin ceto wadanda suka tsira daga mahaukaciyar guguwar Freddy a ranar Laraba yayin da adadin wadanda suka mutu ya haura 270 sakamakon guguwar mai karfi da ta afkawa yankin kudancin nahiyar Afirka.
Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu ya ce shan kaye da wasu jiga-jigan jam’iyyarsu suka yi a zaben 25 ga watan Fabrairu 2023, abin a yaba ma jam’iyyarsu ne bisa shirya zabe na gaskiya.
China ta soki matakin da gwamnatin Biden ta dauka na amincewa da cinikin dala miliyan 619 na sayar wa Taiwan makamai wanda ya hada da daruruwan makamai masu linzami na jiragen yakin F-16, da wasu rahotanni
Tun bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasar Najeriya da hukumar INEC ta yi a makon jiya ne ‘yan kasar na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan irin hasashen fa fatar da suke da shi ga zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Hukumar kula da samar da abinci ta MDD ta tallafa wa ‘yan gudun hijirar cikin gida a jihar Tilabery ta Jamhuriyar Nijar da kudade da nufin sassauta wahalwalun da suka shiga na tserewa daga matsugunansu na asali sanadiyar aika-aikar ‘yan ta’addan arewacin Mali.
Yayin da ake ci gaba da tunkarar zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi a Najeriya, matasa, kungiyoyin fafutuka da wasu masu ruwa da tsaki a harkokin zabe da siyasa sun yi jan hankali ga 'yan kasar musamman ma matasa da su nisanci duk wani wanda zai jawo su cikin yanayi na bangar siyasa.
A cikin shirin na wannan makon mun tattauna ne akan makanta ko rashin gani da wasu cututtuka ke haddasawa wanda kuma za'a iya kaucewa aukuwar hakan
Hukumomin Najeriya sun mika wata ‘yar kasar da ake nema ruwa a jallo ga hukumomin Italiya wacce tun a shekarar 2010 ake nema ruwa a jallo, bayan hukuncin daurin shekaru 13 da aka yanke mata a Italiyar.
Domin Kari