Gwmnatin mulkin sojan Mali ta sanar da yin afuwa ga wasu sojojin Côte d’Ivoire 49 da ta kama a lokacin da suka sauka a filin jirgin saman Bamako a watan Yulin 2022.
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya wato DSS, ta ce bata wani yunkuri don cafke shugaban hukumar zaben kasar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu
Wasu ma’aikatan gwamnati da kuma wata kungiya mai zaman kanta a Ghana sun dauki nauyin yiwa dubban mutane masu fama da matsala ta ido, aikin ido a kasar, da wasu rahotanni.
Daga cikin matakan har da hana shigowa da tsuntsaye daga tarayyar Najeriya, inda a ke ganin daga nan ne cutar ta bullo.
Kotun daukaka kara da ke zama Sokoto ce, ta tabbatar da cewa jam'iyyar ta PDP, za ta iya yin takarar gwamna a zaben da za a yi bana.
Kasar Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijar tallafin jirgin sama samfarin C 130 domin karfafa gwiwa ga sojojin kasar a yakin da suke kafsawa da ‘yan ta’addan yankin Sahel.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar an gudanar da zaben 2023 cikin adalci inda za a damka ragama ga wanda mutane su ka zaba.
Yau aka yi jana’izar Fafaroma Emeritus Benedict na 16, wanda ya rasu yana da shekaru 95 a ranar 31 ga watan Disamba, a birnin Vatican, bayan nan magajinsa Fafaroma Francis zai shugabanci wata hidima da za a gudanar.
Tuni dai wannan al’amari ya haddasa mutuwar dubban kaji, abin da ya sa mahukunta suka dauki matakai don dakile yaduwar cutar.
A cikin shirin na wannan makon mun duba yadda tarihin yankin Arewa ya ke a baya, inda mutane kan taimakawa juna ta hanyar karbar baki, kyautata wa makwabta, tallafawa marayu da sauran su.
Najeriya za ta ci gaba da ba da tallafin man fetur har zuwa tsakiyar shekarar 2023 sannan ta ware Naira tiriliyan 3.36 (dala biliyan 7.5) don wannan bukatar, ministar kudi Zainab Ahmed ta ce.
Masana kiwon lafiya na ganin akwai bukatar yin wani abu cikin hanzari don kula da lafiyarsu, ko da za'a samu biyan bukatar wanzar da kiyon lafiya ga kuwa.
Kungiyar matasa ta Nijar da AJIKAD Nijar, da kuma kungiyar matasan Nijar Musulmi, sun shirya wani taro tare da jami'an tsaron kasar domin neman hanyoyin samarwa matasan dauki game da maganar ta'adanci da tabarbarewar tarbiya.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, ya umarci al’ummomin jihar da su kashe masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’addan da suke yankunansu. Gwamnan yayi wannan ikrari ne a garin Rimi dake yankin karamar hukumar Alkaleri.
Ibtila'in fashewa a garin Appiate da rikicin kabilanci a garin Bawku, yarjejeniya da asusun lamuni na duniya (IMF), ce-ce-ku-cen tsige Ministan Kudi, hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa. zanga-zangar kungiyoyin kwadago da na farar hula.
A karshen shekarar 2022 ne shugaban Amurka Joe Biden ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka kimanin hamsin a Washington DC, inda ya sanar da tallafin dala biliyan 55 ga kasashen Afirka a fannoni da daban-daban cikin shekaru uku masu zuwa, da wasu rahotanni
Pope Emeritus Benedict na XVI (16), Fafaroma na farko da ya yi murabus cikin shekaru 600, ya rasu yana da shekara 95.
Masu sha’awar kwallon kafa a Jamhauriyar Nijar kamar sauran takwarorinsu na sassan duniya sun bayyana alhini a game da rasuwar fitaccen dan kwallon Brazil Pele.
Shaharraren tsohon dan kwallon kafar kasar Brazil, Pele, ya rasu a yau bayan ya yi fama da jinya.
Domin Kari