Kungiyar Gwamnonin Jam’iyar PDP G-5 ta kai ziyara wa Gwamnan Jihar Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Muhammed, a matakin nemo hanyar sulhunta rikicin dake neman kawo baraka a tsakanin gwamnonin da kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyar.
MANUNIYA: Matsayin Shugabannin Fulanin Najeriya Game Da Zaben 2023, Nuwamba 11, 2022
A ranar 15 ga watan Disamba za a fara amfani da sabbin takardun kudin CFA a yankin Afirka Ta Tsakiya. Wannan shawarar an yanke ta ne a ranar 7 ga watan Nuwamba da muke ciki.
Wata babbar kotun birnin tarayya ta yankewa Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC hukuncin zama a gidan kaso sabili da gazawar hukumarsa na kin bin umarnin kotu na baya.
Kungiyoyin rajin demokaradiyya da shugabanci na gari a Najeriya da Jam’iyyun hamayya sun bukaci rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta sanar da Jama’a halin da ake ciki game da wani dan Jam’iyyar APC da ‘yan sanda suka kama da katunan zabe fiye da dari uku.
An yi garkuwa da wani limamin cocin Najeriya daga gidansa da ke arewacin Jihar Kaduna a Najeriya, in ji wata sanarwa da kungiyar darikar Katolika ta fitar a ranar Talata, a karon farko da aka samu rahoton sace wani malamin addini a Jihar tun watan Yuli.
Amurkawa sun kada kuri'a a zaben rabin wa'adi na farko karkashin shugabancin Joe Biden, inda ake sa ido sosai kan yadda zaben sai tabbar da jam'iyar da ke da iko a Majalisa, kujerun gwamnoni da sauran manyan zabuka.
Bankin Duniya ya fitar da rahotonsa na Afirka, inda ya ce, kasar Ghana na daya daga cikin kasashen da aka fi samun hauhawar farashin kayan abinci mafi girma a yankin kudu da hamadar Sahara a shekarar 2022, da wasu rahotanni
Mataimakin sifeton ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta daya da ke Kano ya umarci kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano ya gudanar da kwakkwaran bincike game da cin zarafin da shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado Doguwa, ya yi wa wakilin jaridar Leadership.
Dubban ‘yan Najeriya marasa lafiya ne ke cikin adadin marasa lafiya miliyan daya da rabi daga kasashe 42 da ke cin gajiyar ayyukan kula da lafiya kyauta daga likitocin da ke yawo kasashen duniya don bayar da agajin kiyon lafiya.
Dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, zai kaddamar da kamfen a ranar 15 ga watan Disamba a Jihar Filato bayan tsawon lokaci tun bude kamfen da hukumar zabe ta yi a ranar 28 ga watan Satumba.
An kafa makarantar ne a wani bangare na matakan shigar da nakasassu a sha’anin ilimin boko ta yadda za su tashi da tunanin rungumar kwakkwarar madogarar rayuwa a maimakon shiga harakar bara.
Yayin da wasu kasashen duniya ke fuskantar kalubale ta fuskoki daban-daban, masana sun ce akwai mafita ga kowane irin kalubale da ake fuskanta a duniya.
Sama da tan miliyan tara na shinkafa ne ake shigowa da shi a yankin yammacin Afirka, wanda ke lakume kusan dala biliyan 3.4 a cikin lissafin kudin shigowa da kaya a shekarar 2021.
Batun sauya fasalin kudin Najeriya da babban bankin kasar ya ce zai yi yana ta janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin kungiyoyi masu zaman kansu da ma manazarta a harkokin kudi, musamman ma akan lokacin da bankin na CBN ya bayar.
Kan lamuran tsaro, Kwankwaso ya ce zai kara yawan jami’an sojoji zuwa miliyan daya haka nan ‘yan sanda ma za su zama miliyan daya.
A daidai lokacin majalisar dokoki ta kasa a Nijar ke zaman taron duba kasafin kudin shekara ta 2023, gwamnatin kasar ta ce, za ta kashe sama da biliyon 96 na sefa domin gina ajujuwan karatun boko na dindindin.
A hira da Muryar Amurka a Kano, Manjo Almustapha, ya ce kokarin batawa Abacha suna ne ya sa ake ci gaba da alakanta shi da wadancan kudade shekaru 22 bayan rasuwarsa.
Domin Kari