Shedun gani da ido da kuma 'yan sanda sun ce wani harin bam da aka kai a wani masallaci a birnin Kabul na kasar Afganistan, yayin da ake sallar magariba, ya kashe mutane akalla 21, ciki har da wani fitaccen malamin addini, tare da jikkata wasu akalla 33.