Hakan na nufin zai maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu wanda Buhari ya nada a ranar 15 ga watan Janairun 2019.
Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa an sako dalibai 5 daga cikin 39 da aka yi garkuwa da su a kwalejin horar da ilimin gandun daji da ke jihar.
Madrid za ta je wasan ne da zaratan ‘yan wasa 21, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin.
Akalla 'yan majalisar dokokin Najeriya shida ne suka rasu a majalisa ta 9 (mai zauruka biyu) wacce aka rantsar da mambobinta a ranar 11 ga watan Yunin 2019.
Dan wasan kungiyar kwallon kafar Leicester City, Kelechi Iheanacho ya tswaita zamansa a kungiyar da shekara uku.
A ranar Laraba 31 ga watan Maris jirgin saman Najeriyar ya yi batan dabo, bayan da ya kauce daga kan na’urar da ke bibiyar zirga-zirgar jiragen sama.
Yayin da aka rantsar da Bazoum Mohamed a matsayin sabon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, masu lura da al’amuran siyasa na ganin akwai wani babban kalubale, baya ga na hare-haren 'yan ta'adda da na tattalin arziki da ke gabansa – sabon rikicin siyasar kasar da zaben ya haifar.
Kwana biyu bayan bata dabo da jirgin saman yakin Najeriya ya yi a yankin jihar Borno da ke arewa masa gabashin Najeriya, har yanzu ba a gano inda jirgin yake ba, wanda ke dauke da matuka biyu.
A ranar 6 ga watan Afrilu, Real Madrid za ta gwada kaiminta da Liverpool a zagayen farko na wasannin kusa da na karshe a gasar ta UEFA.
Rahotanni sun ce kotun ta tura su gidan yarin ne don su yi zaman jira, gabanin ta karbi shawarwari daga ma’aikatar shari’ah ta jihar Nejan.
Kasashen duniya ba za su lamunta da duk wani sauyin gwamnati ta hanyar amfani da karfin tuwo ba, domin hakan ba shi da hurumi a kundin tsarin mulki, in ji shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Wannan al’amari na faruwa ne kwana biyu gabanin a mika mulki ga zababben shugaban kasa Mohamed Bazoum wanda zai gaji shugaba Issoufou Mahamadou mai barin gado.
Dan wasan tsakiya na kungiyar Napoli, Victor Osimhen ne ya fara zura kwallo kafin a je hutun rabin lokaci.
An jima rabon da a ga shugaban na Najeriya ya je kasar ta Burtaniya domin duba lafiyarsa.
Ga dukkan alamu, ziyarar da tsohon gwamnan jihar Legas Ahmed Bola Tinubu ya kai Kano inda aka shirya taron tattaunawa don zagayowar ranar haihuwarsa yayin da ya cika shekara 69, ta ta da kura.
Dan wasan Super Eagles Alex Iwobi, ya warke daga cutar coronavirus da aka gano ya kamu da ita gabanin wasansu da Benin a Porto Novo.
Tafiyar ta Buhari na zuwa ne yayin da kungiyar likitocin kasar ta bayyana shirinta na shiga yajin aiki a ranar Alhamis, idan har ba a biya mata bukatunta ba.
‘Yan wasan Crocodiles na kasar Lesotho za su kara da takwarorin wasansu na Super Eagles na Najeriya a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka wanda za a yi a Kamaru.
Kungiyar Likitocin Najeriya ta (NARD,) ta yi barazanar tsunduma yajin aiki na gama-gari a ranar Alhamis mai zuwa muddin gwamnati ba ta cika mata alkawaran da ta yi ba.
Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagora a jam’iyyar APC mai mulki Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya isa birnin Kano domin wata ziyara ta musamman.
Domin Kari