Kungiyoyin Manchester United da Liverpool na shirin gwada kaiminsu a ranar Lahadi a ci gaba da gasar Premier League ta Ingila.
Rahotanni daga jihar Kogin Najeriya na cewa, masu garkuwa da mutane da suka sace wasu ‘yan kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, sun nemi a biya su kudaden fansa.
Dan wasan Brazil Neymar da ke taka kwallo a kungiyar PSG ta kasar Faransa, yana kan tattaunawa da hukumomin kungiyar don ganin yadda zai tsawaita zamansa a kungiyar.
Manchester United ta zauna daram a saman teburin gasar Premier League ta Ingila bayan da ta doke Burnley da ci 1- 0.
Hukumar NCDC da ke yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce mutanen da cutar COVID-19 ta harba a kasar, sun haura 100,000.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PNDS mai mulki Mohamed Bazoum zai kara da tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane na jam’iyyar RDR a zaben zagaye na biyu da za a yi a watan Fabrairu.
Hukumar zabe ta CENI a Jamhuriyar Nijar ta ce babu dan takarar da ya samu kashi 51 na kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 27 ga watan Disambar bara.
Hukumar zabe ta CENI a Jamhuriyar Nijar, ta ce ana gudanar da zabe a yau Litinin 28 ga watan Disamba a yankin Madama da ke jihar Agadez.
Ofishin jakadancin Amurka da ke Yamai, babban birnin Nijar, ya yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki cikin lumana.
Da safiyar yau shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar ya kada kuri’arsa a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da ake yi a Nijar.
A ranar Lahadi 27 ga watan Disamba al’umar Nijar za ta yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki, inda hankulan mutane ya fi karkata kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, tsaro da kuma annobar coronavirus.
Jamhuriyyar Nijar kasa ce da ke yammacin Afirka wacce ke bin tafarkin dimokradiyya. Tana bin tsarin shugabanci wanda iko da umurni ke gudana daga gwamnatin tsakiya.
Tsohon shugaban hukumar fansho a Najeriya Abdulrasheed Maina da ake tuhuma da wawure biliyoyin kudade, ya yanke jiki ya fadi yayin da kotu ke sauraren kararsa a Abuja.
Kotun da ke sauraren karar Abdulrasheed Maina, wanda ya jagoranci tsohon kwamitin yin garanbawul ga fannin fansho a Najeriya, ta ba da umurnin a rufe shi a gidan yari.
Kungiyar Kwallon kafa ta Nice da ke wasa a gasar Ligue 1 ta kasar Faransa ta sallami kocinta Patrick Vieira.
Cristiano Ronaldo wanda dan asalin kasar Portugal ne ya zira kwallonsa ta 750 cikin shekarun da ya kwashe yana buga tamaula.
Kotun tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta zanawa Sanata Ali Ndume wasu sharudda da zai aiwatar kafin ta ba da belinsa.
Ana zaman dar-dar yayin da al'umar yankin Tigray ke ficewa daga gidajensu domin gujewa harin karshe da dakarun Ethiopia ke shirin kai wa.
‘Yan wasan Liverpool Mohamed Salah da Sadio Mane sun shiga jerin ‘yan wasa 11 da ke neani kambun zama zakaran duniya na FIFA a bangaren maza.
Tsohon dan wasan kwallon kafa na Najeriya Daniel Amokachi ya bi sahun takwarorinsa a fagen wasan kwallo wajen nuna alhinin mutuwar shahararren dan wasa Diego Armando Maradona.
Domin Kari